Nigeria TV Info
CBN ta Haramta Wa Manyan Masu Kin Biyan Bashi Samun Sabbin Lamuni a Najeriya
Babban Bankin Najeriya â Central Bank of Nigeria (CBN) â ya bayar da umarni ga bankuna da su hana manyan âyan kasuwa da kamfanoni da ke kin biyan bashin su samun sabbin lamuni ko wasu muhimman ayyukan banki. Wannan mataki na nufin wadanda aka bayyana a matsayin largeâticket obligors da ke da bashin da ba a biya ba ba za su iya samun wasu bashi ba har sai sun biya na da su gaba Éaya.
A cikin wata wasika da aka fitar ranar 12 ga Maris, 2026, CBN ta umurci dukkan bankunan kasuwanci da su dakatar da ba wa waÉannan masu bashin sabbin abubuwa kamar lamuni, tabbacin banki (bankersâ confirmations), wasikar lamuni (letters of credit), garanti aiki (performance bonds) da sauran su.
Bankin ya ce wannan umarni na zuwa ne domin Æarfafa tsarin biyan bashi, rage hatsarin da rashin biyan bashi ke jawowa tsarin kuÉi, da kuma tabbatar da cewa masu bashi suna bin dokokin bashi yadda ya kamata.
CBN ya kuma ba da shawara bankuna su Æara samun karin jinginar dukiya (collateral) daga waÉanda ke da bashin da ba a biya ba domin kare kuÉaÉen da suke rike da su.
Bankin ya yi gargadi cewa bankunan da suka saba wannan umarni za su fuskanci hukunci bisa dokar Banks and Other Financial Institutions Act (BOFIA) 2020.
Sharhi