A safiyar Lahadi, wasu 'yan bindiga sun farmaki kauyen Hayin Gizo da ke yankin Garun Kurama a karamar hukumar Lere, jihar Kaduna, inda suka sace mutane shida.
Wani mazaunin kauyen ya bayyana cewa maharan sun iso kauyen da misalin karfe 1:30 na dare, suna harbe-harbe da razana mazauna garin. Harin ya dauki kusan sa'o'i biyu.
Cikin wadanda aka sace akwai 'yan kasuwa biyu 'yan kabilar Igbo da kuma wasu manoma na kauyen. Wata mace da aka sace tun da fari an sake ta saboda rashin lafiyarta.
Mazauna yankin sun bayyana cewa wadanda aka sace manoma ne da ke fama da rayuwa, kuma ba su da halin biyan kudin fansa. Sun roki 'yan bindigar da su nuna tausayi, tare da kiran hukumomin tsaro da su dauki matakin gaggawa.
Yankin Lere da makwabtansa kamar Kauru, Kachia, Zango Kataf da Jema’a na fuskantar karuwar hare-haren 'yan bindiga da sace-sace a 'yan watannin baya-bayan nan.