Ma’aikatar Muhalli ta ƙaddamar da yaƙin neman dafa abinci mai tsafta da raba murhun zamani a duk faɗin Najeriya domin inganta lafiyar gida da kariyar muhalli.
An fara aiwatarwa a jihohin Ebonyi da Kebbi, inda ake amfani da murhun da aka ƙera cikin gida wanda ke rage hayakin dafa abinci da sare dazuka da fitar da hayaƙin gurbata yanayi.
Dr. Iniobong Abiola-Awe wacce ta wakilci Minista Balarabe Abbas Lawal, ta jaddada muhimmancin shigar da shugabannin al’umma, mata, matasa da nakasassu. Ta kuma bayyana cewa shirin yana bai wa ‘yan kasuwa horo da kayan aiki.
Shirin yana taimakawa lafiyar jama’a, kare muhalli da bunkasa tattalin arziki, tare da taimakawa Najeriya wajen cimma yarjejeniyar Paris da manufofin cigaban SDG na Majalisar Dinkin Duniya.