Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, na iya kawo ƙarshen yaƙin da Rasha nan take idan ya daina neman Crimea da kuma burin shiga NATO.
“Zelensky zai iya kawo ƙarshen yaƙi da Rasha idan yana so, ko kuma ya ci gaba da faɗa. Ku tuna yadda komai ya fara. An ɗauki Crimea ba tare da harbi ba shekaru 12 da suka wuce, Ukraine kuma ba ta shiga NATO ba. Wasu abubuwa ba sa canzawa!!!” Trump ya rubuta a Truth Social.
Ya kuma ƙara da cewa Litinin zai kasance “rana mai girma” ga White House saboda ba a taɓa ganin shugabannin Turai da yawa a lokaci guda ba.
Sharhi