Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta rika biyan daliban da ke halartar kwalejojin fasaha a fadin kasar Naira 45,000 a kowane wata.
Shugaban hukumar NBTE, Farfesa Idris Bugaje, ne ya bayyana haka a hira da NAN a Abuja.
Ya ce, wannan shirin zai kara janyo hankalin matasa zuwa makarantar fasaha don koyon sana’o’i, samun aiki a cikin gida da kasashen waje.
Ya kara da cewa wannan mataki wani sabon farawa ne ga bangaren TVET wanda aka fara mantawa da shi tun daga shekarun 1980.
Ya jaddada cewa N45,000 din ba aro ba ne, kyauta ce wadda daliban ba za su mayar da ita ba. Burin gwamnati shi ne kara jawo mutane su shiga ilimin fasaha.