LABARI NA GAGGAWA: Saudiyya ta bayar da agajin ido kyauta ga mutane 4,000 a Lagos

Rukuni: Labarai |

Gwamnatin Saudiyya, ta hanyar cibiyar agaji ta Sarki Salman (KSrelief), ta bayar da agajin ido kyauta ga mutane 4,000 a garin Lagos.

Tunda aka kaddamar da kamfen din hana makanta a Najeriya tun 2019, KSrelief ta yi gwajin ido fiye da 218,000, ta raba gilashin ido fiye da 45,000, kuma “fiye da mutane 21,000 sun dawo da ganinsu ta hanyar tiyata”.