Ƙungiyar Concerned Christian Youth Forum (CCYF) ta shirya gudanar da zanga-zangar lumana a ranar 21 ga Mayu a Unity Fountain, Maitama, Abuja daga karfe 10 na safe zuwa 2 na rana. Zanga-zangar na nuna rashin jin daɗin yadda ake ƙara kai hari kan addinin Kirista da shugabanninsa.
Jagoran ƙungiyar, James Paul Adama, ya ce suna zargin Omoyele Sowore da abokan aikinsa da ƙoƙarin tayar da rigimar addini. Ya ce, “Addininmu yana fuskantar barazana. Wannan shiri ne da aka tsara domin raba kan al’umma.”
CCYF na kuma neman gwamnati ta dauki mataki kan yawaitar kashe-kashe a ƙasar. Za a samar da motocin daukar nauyin masu halarta daga sassa daban-daban na Abuja da ƙananan hukumomi shida na FCT.
An bukaci matasan Kiristoci su halarta domin bayyana damuwarsu da kare imanin su.