Sabon aron $24bn na iya haifar da hauhawar bashin Najeriya zuwa N183tn

Rukuni: Labarai |

28 ga Mayu, 2025

Shugaba Bola Tinubu

•Majalisar dokoki ta kasa na dab da amincewa da bukatar rancen Tinubu, bashin waje ya kusa $70bn, masana tattalin arziki na nuna damuwa kan yadda ake biyan bashi

Ana sa ran bashin Najeriya zai sake karuwa sosai yayin da Shugaba Bola Tinubu ya bukaci amincewar majalisar dokoki ta kasa domin samun sabon rancen kasashen waje da ya kai kimanin $24.14bn.

Da amfani da sabon farashin musayar hukuma na N1,583.74/$1, wannan aron zai kara kusan N38.24tn zuwa bashin da ake da shi a yanzu, wanda zai iya kai bashin Najeriya daga N144.67tn a ƙarshen 2024 zuwa sama da N182.91tn a shekarar 2026.

Sabon rancen ya kunshi $21.54bn, €2.19bn da ¥15bn. Bisa sabon farashin kasuwa—€1 zuwa $1.1381 da ¥1 zuwa $0.0068—sashin euro ya kai kusan $2.5bn, yayin da yen na Japan ya kai $102m.